Jam’iyyar ADC ta nuna takaici matuƙa kan rahoton karɓar haraji na naira miliyan 56 daga manoma a Jihar Zamfara da ƴan bindiga suka yi, tare da hoton faifan bidiyon wani ƙauye a Ifelodun Jihar Kwara, da ƴan ƙauyen suka fice baki ɗaya saboda tsoron hare-hare.
A cewar Mallam Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar, wannan lamari ba wai kawai na nuna rashin tsaro bane, “amma gargaɗi ne ga ƙasa baki ɗaya.”
Ya bayyana cewa idan ƴan ta’adda za su iya karɓar kuɗi daga manoma don ba su damar shiga gonakinsu, to hakan yana nuna sun shiga fafatawa da gwamnati wajen mulkin wani ɓangare na ƙasa.
“Idan ƴan bindiga na iya karɓar haraji daga ƴan ƙasa da bindiga, to gwamnati ta miƙa wuya kenan,” in ji shi cikin zazzafar magana.
Jam’iyyar ta tuna da maganar Tinubu a 2014 lokacin yana adawa, inda ya ce “idan kana da ikon jagorantar sojoji, me yasa wani yanki na ƙasa zai kasance ƙarƙashin mamayar wasu?”
Sai dai yanzu matsalar tsaro ta ƙaru ƙwarai a ƙarƙashin jagorancin Tinubu, amma babu wanda ke kiransa da ya yi murabus.
ADC ta yi kira ga shugaban ƙasa da ya daina jan ƙafa, ya mai da hankali kai tsaye kan Zamfara da sauran wuraren da ke fama da ƴan bindiga a ƙasar nan.
Tana zargin cewa rashin ɗaukar mataki daga fadar shugaban ƙasa na ƙara baiwa miyagu damar samun ƙarin ƙarfi.
Masu lura da harkokin tsaro sun ce wannan wani sabon yanayi ne na “gazawar ƙasa” da zai iya bazuwa zuwa wasu sassan da ake ganin suna da kwanciyar hankali.