Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta nuna damuwa matuƙa kan yadda aka gudanar da zaɓukan cike-gurbi na Asabar, 16 ga Agusta, a jihohi 12 da mazaɓu 16, tana mai cewa tsarin zaɓe ya ƙara lalacewa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu da APC.
A cewar mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, zaɓukan sun cika da rahotannin samun tashin hankali, sayen ƙuri’u, maguɗi, da kuma manyan kura-kurai na gudanarwa.
ADC ta jaddada cewa ba ta tsaya takara a mafi yawan kujerun ba, don haka wannan zaɓe “bai kamata a ɗauke shi matsayin auna ƙarfin kawancen adawa ba,” sai dai abin da ke nuna “yadda aka karkatar da tsarin kan abin da ya saɓa da muradin jama’a.”
Sanarwar ta ce, “Abin da ƴan Najeriya suka gani a zaɓen jiya shine wata shaida ta cewa demokaraɗiyya a wannan gwamnatin tana ci gaba da ci baya ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da APC.”
Ta Ƙara bayyana cewa, “Duk lokacin da aka ce zaɓe ya cika da tashe-tashen hankula . . . kuma duk lokacin da aka ce hukumomin da ke da alhakin kare demokaraɗiyya suka zama masu daƙushe ta, to zaɓin ɗan Najeriya ya zama marar amfani,” tare da ƙari da cewa: “Shin wannan demokaraɗiyya ce ko ta’addanci aka ɓoye a cikin zaɓe?”
Jam’iyyar ta kawo misalan kama kusan “ƴan bangar siyasa 300” a wasu jihohi, soke rumfunan zaɓe saboda satar akwatunan jefa ƙuri’u da razanar da masu kaɗa ƙuri’a, da kuma kama wani “mai sayen ƙuri’u . . . da naira miliyan 25.9,” tana cewa “Wannan ba ɓoyayyen maguɗi ba ne, ya zama al’adar siyasa . . . a ƙarƙashin APC” tare da jan kunnen INEC cewa “Bai taɓa kamata a bar INEC ta koma wajen neman uzuri ba.”
A ƙarshe, ADC ta roƙi Shugaba Tinubu ya “manta da jam’iyyancinsa” ya tabbatar da zaɓe mai ƴanci da tsaro, domin gwamnati ba za ta samu “inganci” ba idan ana ci gaba da zaɓukan da jama’a da ƙasashen duniya ke kallon su a matsayin na bogi.