Wasu ƴanbindiga da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mata ashirin da uku a garin Damaga na Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin, Malam Ahmed Mohammed ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da DAILY POST ta wayar salula a daren jiya Alhamis.
Ya ce, lamarin ya faru ne ranar Laraba da tsakar rana, misalin ƙarfe sha biyu, lokacin da waɗanda lamarin ya rutsa da su suka shiga daji domin yiwowa itace.
Mafi yawan matan ƴanmata ne da kuma zawarawa, sai dai kuma ƴanbindigar sun saki ƙananan yaran da suke tare da su.
Labari Mai Alaƙa: An Kama Ƴan Boko Haram Da Ke Kitsa Kai Hari Gidan Atiku
Ƴanbindigar sun kuma kai hari garin Talata Madara, shalkwatar mulki ta Ƙaramar Hukumar Madara a dai Jihar ta Zamfara inda sukai garkuwa da ma’aikata goma na kamfanin yin titi mai suna, Triacta.
Wani mazaunin garin, Malam Abdulrahman Yusuf ya bayyana cewa, ƴanbindigar sun shiga garin ne da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare a ranar Larabar da ta gabata.
Ya ƙara da cewa, sun wuce kai tsaye zuwa gidan tsohon Ɗan Majalissar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Talata Madara da Anka, Hon. Kabiru Calssic.
To sai dai kuma daga bisani, sojoji sun sami nasarar korar ƴanbindigar bayan sun ɗebe awa ɗaya da rabi suna cin karensu babu babbaka a garin.