Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya gabatar da sunayen mutane 11 da suka kai matakin karshe na zaɓen manyan sakatarori, PS, kamar yadda wata takarda ta nuna.
Takardar, wadda Dr. Emmanuel Meribole ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa daga cikin manyan daraktoci 19 da suka yi nasarar wucewa mataki na biyu na jarrabawar, mutum 11 ne za su halarci tambayoyin kai tsaye kan neman matakin.
Wannan mataki ne na cigaba a wajen cike guraben manyan sakatarori daga jihohi takwas.
A watan Oktoban da ya gabata, jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an fara shirin ɗaukar ma’aikatan ne tare da daraktoci 38 da suka shiga matakin farko na jarrabawar.
Daga ciki, mutum 19 sun kai mataki na biyu, yayin da 11 ne suka samu zuwa mataki na uku.
A wata takarda daban da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta sanya wa hannu, an haramta wa daraktocin da ke fuskantar hukunci shiga takarar, don tabbatar da tsauraran ka’idojin tantancewa.
Shugaba Bola Tinubu ne ya amince da wannan aikin, kuma za a bayyana sunayen waɗanda suka yi nasara a karshen tantacewar.