Ƴan Najeriya 9 Da Aka Tabbatar Da Sunayensu Don Karɓar Kyautar Ballon d’Or

Kyautar Ballon d’Or ce mafi girman nasarar kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa, wadda ake bayarwa duk shekara ga mafi kyawun ‘yan wasa mata da maza a duniya.

Tun daga kafuwarta a shekarar 1956, ta zama alamar babbar lambar yabo da kowane ɗan wasa zai iya samu.

Ƙalilan ne daga cikin ‘yan wasan Najeriya da aka taɓa tabbatar da sunayensu don wannan kyauta.

Karo na farko da ‘yan Najeriya suka samu wannan lambar yabo ya kasance a shekarar 1995, lokacin da aka tabbatar da sunayen Finidi George, Daniel Amokachi, da Austin Jay-Jay Okocha domin karɓar kyautar.

Wannan yabo ya nuna bajintarsu kuma ya buɗe ƙofa ga sauran ‘yan wasa ‘yan Afrika a fagen duniya.

Nwankwo Kanu ya samu lambar yabon sau biyu – karo na farko a 1996 lokacin yana Arsenal, sannan a 1999 yana wasa da Inter Milan.

A shekarar 1997, Victor Ikpeba ya samu tabbacin karɓar kyautar lokacin da yake AS Monaco, sannan Sunday Oliseh a shekarar ya samu a 1998 lokacin da yake Juventus.

Wadannan ‘yan wasan sun kafa tarihi a duniya, sun wakiltar Nahiyar Afrika da kyau, sannan kuma sun zama abin koyi ga matasan ‘yan wasa.

A 2023, Victor Osimhen da Asisat Oshoala sun shiga cikin jerin ‘yan wasan Najeriya da aka tantance, kuma sun kafa tarihi a matsayin namiji da mace na farko daga Najeriya da aka ambata a wannan shekarar.

Osimhen ya samu wannan lambar yabo saboda bajintar da ya nuna a Napoli, inda ya zura kwallaye 26 a gasar Serie A.

Ita kuma Oshoala ta samu yabon saboda taimakawa kungiyarta ta Barcelona ta lashe gasar zakarun mata ta Champions League da kuma gasar La Liga.

A shekarar 2024, Ademola Lookman ya samu shiga cikin jerin ‘yan wasa 30 da aka tabbatar don kyautar Ballon d’Or, bayan nasarar da ya samu a gasar Europa League inda ya zura kwallaye uku a wasan karshe da suka yi da Bayer Leverkusen.

Ƴan Najeriya 9 Da Aka Taba Tantance Su Don Kyautar Ballon d’Or

– Finidi George (1995)

– Daniel Amokachi (1995)

– Austin Jay-Jay Okocha (1995)

– Nwankwo Kanu (1996, 1999)

– Victor Ikpeba (1997)

– Sunday Oliseh (1998)

– Asisat Oshoala (2022, 2023)

– Victor Osimhen (2023)

– Ademola Lookman (2024)

Ballon d'OrWasanni
Comments (0)
Add Comment