Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe Tsohuwar Matarsa Da Ɗan Fashi A Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan kai da fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.

Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa Iliyasu Musa, mai shekaru 40 daga ƙauyen Ɗangewaye, an kama shi bisa zargin kashe tsohuwar matarsa, Hadiza Sale, mai shekaru 30 daga Afasha.

An ce ya buge ta da sanda a ka, yayin da take dawowa daga kasuwa da daddare, bayan ya yi mata kwanton ɓauna a kusa da gidanta.

Rundunar ta bayyana cewa “an kama wanda ake zargin ne a ranar 23 ga watan Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani inda yake ɓoye,” kuma yanzu yana hannun SCID Dutse don ci gaba da bincike.

WANI LABARIN: Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Nuna Wariya Ga Yankin Arewa

Haka kuma, an kama wani mai suna Alpha Samaila, mai shekaru 20 daga Sabuwar Unguwa, bisa zargin shiga gidan wani Abubakar Yahaya da rana tsaka, ya farmasa da wuƙa tare da sace masa naira 170,000 da waya Techno Hot 40i.

“An kai wanda aka farmasa asibitin kula da lafiya na farko a Roni domin jinya kafin daga bisani aka sallame shi,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Kwamishinan ƴan sanda Dahiru Muhammad, ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa tare da jaddada cewa “rundunar ba za ta yarda da masu laifi su samu mafaka a jihar ba.”

Comments (0)
Add Comment