Ɗan El-Rufa’i Da Ƴar Ibori Sun Sami Shugabanci A Yayin Majalissar Wakilai Ta Fitar Kwamitoci

Mohammed Bello El-Rufai, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i da Erhiatake Ibori-Suenu, ƴar tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori sun sami shugabancin kwamitocin dindindin na Majalissar Wakilai a yau Thursday.

Kakakin Majalissar Wakilan, Tajuddin Abbas ya sanar da kwamitocin dindindin 134 a zaman majalissar na yau Alhamis.

Labari Mai Alaƙa: DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Miƙawa Sanatoci Sunayen Ministoci, Sunan Badaru Ne Daga Jigawa

Ya sanar da sunan ƴar gidan James Ibori a matsayin shugabar Kwamitin Majalissar kan Hukumar Raya Yankin Niger Delta, NDDC, yayinda shi kuma ɗan El-Rufa’i ya zama shugaban Kwamitin Majalissar Kan Harkokin Banki.

Su ma tsohon Mataimakin Kakin Majalissar, Ahmed Idris Wase, da tsohon Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Ado Doguwa, da Yusuf Adamu Gagdi, da Mukhtar Betara sun samu muƙaman shugabancin kwamitoci.

Kwamitocin MajalissaMajalissar Wakilai
Comments (0)
Add Comment