Fitar da ɗanyen mai a Najeriya ya fuskanci gagarumar koma baya a watan Satumba, inda aka samu raguwa da ganguna 33,000 a kowace rana, wanda hakan ya saukar da matsakaicin yawan fitar da ɗanyen man zuwa ganguna miliyan 1.405 a kowace rana, a cewar Ƙungiyar Ƙasashen da ke Fitar da Man Fetur wato Organisation of Petroleum Exporting Countries (OPEC).
Rahoton OPEC na watan Oktoba, wanda ya samo bayanai daga hukumomin Najeriya, ya nuna cewa an samu raguwa daga matakin fitar da ganguna miliyan 1.438 da aka samu a watan Agusta.
Ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta wajen samar da fetur ya fito fili, inda ƙasar ke gwagwarmaya wajen cimma yawan man da OPEC ta amince mata da kuma biyan buƙatun matatun cikin gida.
Tun watannin baya dai, Najeriya tana fama da matsalar kiyaye tsayayyen adadin ɗanyen man da take fitarwa.
Haka kuma, tun farkon shekarar nan, alƙaluman fitar da man sun riƙa canzawa, yawanci suna zama tsakanin ganguna miliyan 1.2 zuwa miliyan 1.3 a kowace rana, abin da ke gaza abin da ƙasar ke da damar samarwa.
Masana sun danganta wannan matsala da rashin ingancin ayyuka, lalacewar kayan aiki, da kuma satar danyen mai – matsalolin da suka daɗe suna addabar fannin mai na ƙasar.
Wannan sabuwar raguwa a fitar da ɗanyen man ta nuna irin wahalhalun da Najeriya ke fuskanta wajen cimma samun kudaden man da OPEC ta ɗibar mata.
A shekarun baya, kasar ta sha wuce yawan ganguna miliyan 2 a kowace rana, wanda hakan ke ƙara jefa damuwa kan wannan koma bayan da ake samu a yanzu.
Fannin man fetur na Najeriya, wanda a da yake taka muhimmiyar rawa a kasuwar duniya, yanzu yana fuskantar ƙalubale mai yawa na farfaɗowa bayan shekaru na rashin zuba jari yanda ya kamata da kuma rashin tabbas na kasuwar mai ta duniya.
Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na gudanar da sauye-sauye da kuma janyo masu zuba jari daga ƙasashen waje, samar da fetur a Najeriya bai sake samun cikakken tagomashi ba.
Raguwar da aka samu a watan Satumba ta ƙara sanya Najeriya cikin matsin lamba, musamman yanda ƙasar ke ƙoƙarin samun ƙarin kuɗin shiga daga mai, a lokacin da take fama da matsalolin tattalin arziki.
Fannin man fetur dai na ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arziƙin Najeriya, inda yake ba da gudunmawar kusan kashi 90% na kuɗaɗen da ake samu wajen fitar da kaya zuwa ƙasashen waje, da kuma kashi 50% na kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Sai dai, raguwar da ake samu a fitar da ɗanyen man na zama tasgaro ga damar ƙasar na samun kuɗin musaya da kuma tallafawa wasu ɓangarorin tattalin arziki suna cikin hatsari.
Yayin da Najeriya ke neman dawowa kan matsayinta na baya, tambayar a nan ita ce: Ko za ta iya shawo kan dinbin matsalolin da suka hana ta ci gaba, ko kuwa ƙasar za ta ci gaba da fuskantar koma baya a fannin mai?