Ɗaruruwan Ƴan Boko Haram Sun Tsere Daga Wani Gidan Yari

Ɗaruruwan ƴan ta’adda, ɓatagari da masu safarar ƙwayoyi ne aka rawaito sun tsere daga wani gidan yari a Jamhuriyar Nijar.

Gidan yarin da ke kusa da babban birnin ƙasar, Niamey, ya fuskanci mummunan hari a jiya Alhamis, inda aka rinjayi masu gadinsa tare da samar da dama ga fursunonin da ke gidan domin tserewa da makamai da kuma ababen hawa.

Wani ganau a lamarin ya bayyana cewar, an ji ƙarar harbe-harbe da tashin nakiyoyi a cikin gidan yarin da misalin tsakar dare, abun da ya jawo jami’an tsaro mayar da martani cikin gaggawa.

Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar ya tabbatar da tserewar fursunonin, inda kuma yai kira ga dagatai da shugabannin addini da su sanar da ganin duk wani wanda ake zargi.

Tuni dai aka sanya dokar hana zirga-zirga a yankin Tillaberi, sannan kuma kafatanin yankin Kogin Niger na cikin kulawar tsaro.

Boko Haram
Comments (0)
Add Comment