Ƙara Kuɗin Makaranta; Anya Kuwa Ba A Tsokano Wata Fitinar Ba?

Daga: Hafsat Abubakar Sadiq

A baya bayan nan, ƙarin kuɗin makaranta da aka samu musamman ga ɗaliban wasu Jami’oin Tarayya ya bar baya da ƙura.

Wannan mataki da aka ɗauka, ba kaɗai ɗalibai ya shafa ba, har ma da uwa-uba iyaye. A yayinda har yanzu mafi ƙarancin albashi a Najeriya yake naira dubu talatin, ga matsi na tattalin arziƙi da tashin gwauron zabi da kayan masarufi suka yi, hakan ya sa magidanta ke fafuta matuƙa gaya da abunda za a kai baka a dai-dai lokacin nan ne kuma kuɗin makaranta shima yai tashin gwauron zabin.

Ya kamata a duba wannan lamarin tunda aƙalla ɗalibai ba su da hannu a  taɓarɓarewar ilimin ƙasar nan. Wannan ƙarin kuɗin tamkar  hanya ce ta rage ɗaliban jami’o’i, domin kuwa mafi yawan ɗalibai zasu bar karatunsu a dalilin hakan. Ta yaya ɗalibai zasu  faɗawa iyayensu masu ƙaramin  ƙarfi cewa an ƙara kuɗin makaranta bayan sun san irin fafutukar da suke a kan su sama musu kuɗin makarantar kafin a yi ƙarin? Mutanen da ke wannan rukunin su kan sai da kadarorinsu ne su ƙarƙaf su kai yaransu makaranta, su kuma yi amfani da ɗan kuɗin da suke samu a buge-bugensu na ƙananan sana’o’i su basu kuɗin abinci da da sauran buƙatun da zasu samu na ɗalibai, wanda suke sa ran zasu samu kafaɗar dafawa idan ƙarfinsu ya ƙare bayan kammala karatun yaran nasu. Amma duba da irin yanda yanayin ya sauya lokaci ɗaya akwai yiwuwar samun yawaitar sarewar guiwa ga iyaye da dama da kuma ɗalibai da dama a Najeriya abin da zai iya ƙara jefa ƙasar cikin ruɗani.

Labari Mai Alaƙa: Makaho Bai San Ana Ganin Sa Ba…!

A Zangon da aka kammala ɗalibai sun biya naira dubu 32 zuwa dubu 42, amma a wannan zangon ana maganar dole ne ɗalibai su biya naira dubu 97 zuwa dubu 170. Ɗakin kwanan ɗalibai kuwa ya kasance a baya naira dubu 15 zuwa dubu 23 amma a yau ɗalibai dole zasu biya naira dubu 37 zuwa dubu 57. Abun Tambayar anan shine, idan ASUU ta fara yajin aiki a yau, shin makarantun da suka ƙara kuɗi ban da su a cikin tsarin? Shin makarantun a yanzu Jami’oin Tarayya ne ko masu zaman kansu? Ta yaya muke tsammanin ɗalibai da iyaye za su sami wannan maƙudan kuɗaɗen? Anya ba a buɗe damar aikata ba daidai ba ga wasu masu ƙarancin ƙarfin zuciyar? Anya ba a tsokano wata fitinar ba? Ya kamata hukumomi su faɗaɗa nazari. Babu al’ummar da zata samu ci gaba alhalin mutanenta ba su da ilimi.

Ɗalibai da dama suna jin tsoron dokar bayar da bashi ga ɗalibai wato students loan, saboda wasu manyan ramuka dake tattare da tsarin. Hakan ya tilastawa wasu ɗaliban zuwa wajen manyan gari da ƴan siyasa don neman tallafi daga garesu bayan an yi ƙarin kuɗin, ga shi sabon zangon karatu ya fara tafiya ba su samu sun biya ba – shin zasu fara ɗaukar darasine a yayin da suke jiran tallafin? Me zai faru idan har aka zo jarabawa basu samu tallafin ba? Sai dai su haƙura da neman ilimin kenan su koma gida?

Ya kamata masu riƙe da madafun iko su fahimci cewa, ƙara kudin makarantu ya shafi ci gaban ƴan Najeriya ne gaba ɗaya, wanda dama can suna fama da matsin tattalin arziƙi da ƙarancin walwala da rashin tabbas. Dole ne idan gwamnati tana son ƴan ƙasar nan su ci gaba, su kuma samu damar temakawa ƙasar, ta fitar da tsarukan da za a gamsu da cewar manufofinta na alheri ne.

Bahaushe dai ya ce, gyara kayanka . . .

Daga: Hafsat Abubakar Sadiq

Hafsat Abubakar SadiqTsadar Kudin Makaranta
Comments (0)
Add Comment