Daga Mika’il Tsoho, Dutse
Ƙungiyar bada agaji mai zaman kanta ta Follow the Money, reshen Jihar Jigawa, ta miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa bisa mummunar gobarar tanka da ta auku a garin Majia a makon jiya.
Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na jihar, Malam Adam Sulaiman ya sa wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai, ƙungiyar da ke mayar da hankali kan bin diddigin kuɗaɗen gwamnati da na tallafin ƙasa da ƙasa, ta nuna matuƙar tausaya ga waɗanda suka rasa rayukansu da sauran waɗanda lamarin ya shafa.
“Zuƙatanmu sun kaɗu game da waɗanda bala’in nan ya tarwatsa iyalansu,” in ji sanarwar, tana mai miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu.
Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya ba iyalan mamatan ƙarfin juriya a kan wannan babban rashi da aka yi.
Sanarwar ta kuma yi addu’a ga ran mamatan, tana roƙon samun rahamar Ubangiji ga iyalan su.
“Allah Ya jiƙan waɗanda suka mutu kuma Ya ba iyalansu haƙurin jure rashin,” in ji sanarwar.
A cewar rahoto daga rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon wannan gobarar ya haura 170, yayin da sama da mutum 70 ke jinya a asibitocin Dutse, Kano da Nguru.
Wannan gobarar tanka a Majia tana daga cikin manyan annobar da jihar ta fuskanta a ƴan shekarun nan, tana tuna irin waɗannan bala’o’i da aka sha fuskanta a sassan Najeriya, inda haɗurran tankoki ke haddasa mummunar asarar rayuka da dukiya.
Wannan lamari ya ƙara shiga jerin manyan haɗurra, yana nuna ci gaba a samun ƙalubalen tsaro a kan hanyoyi da kuma shirye-shiryen kai ɗaukin gaggawa a faɗin Najeriya.