Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya Ta Yi Allah-Wadai Da Sabon Tsarin Albashin Gwamnati

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Mata Masu Aiki a Cibiyoyin Lafiya na Tarayya (NANNM-FHI) ta bayyana rashin jin daɗinta game da sabon tsarin albashi da Hukumar Albashi da Kuɗaɗen Shiga ta Kasa ta fitar, inda ta ce an cire su daga muhimman sauye-sauyen samun alawus-alawus.

Shugaban ƙungiyar, Morakinyo-Olajide Rilwan, ya ce wannan takarda wadda aka fitar ranar 27 ga Yuni ba ta nuna kimar da ma’aikatan jinya ke da ita ba, duk da cewa su ne kashi 60 zuwa 70 cikin ɗari na ma’aikatan lafiya.

“Ma’aikatan jinya na aiki a cikin yanayi na gajiya, suna shafe sa’o’i masu tsawo da marasa lafiya da danginsu, amma har yanzu alawus ɗin karɓa-karɓa da muke karɓa bai wuce kashi 8.5 cikin ɗari na albashi ba,” in ji shi.

WANI LABARIN: Ɗan Takara Daga Arewa Ne Kadai Zai Iya Kayar Da Tinubu A 2027, In Ji Wani Lauya Ɗan Kudu

Ya ce sau da yawa ma’aikatan jinya su kan canja kayan aiki har sau uku a rana, amma har yanzu ba a ware musu isasshen alawus na sayen kayan aiki ba.

Rilwan ya bayyana cewa rashin bai wa ma’aikatan jinya alawus irin na ƙwararru babbar wariya ce ga waɗanda suka samu horo na musamman.

Ya kuma jaddada cewa rashin samar da tsayayyen tsari na riƙe ma’aikatan jinya a Najeriya ke sa su guduwa zuwa ƙasashen waje domin neman kyakkyawar rayuwa.

“Muna da ma’aikatan jinya a Najeriya, amma muna rasa su saboda rashin jin daɗin aiki da kuma ƙin ba su kulawa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnati da ta samar da sashen ma’aikatan jinya a cikin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma sake farfaɗo da Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya da Mata Ma’aikatan Lafiya.

Ya ce ƙungiyar za ta ba gwamnati damar duba batun, amma idan ta ƙi ɗaukar mataki, za su ɗauki matakin nuna ƙin amincewa.

Comments (0)
Add Comment