Rahoton Hukumar Kare Ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) na watan Yunin 2025 ya bayyana cewa Najeriya ce ke da yawan ƴan gudun hijira mafi yawa a Yammacin Afirka – da adadi mai ban mamaki na mutane miliyan 8.18 da suka rasa matsugunansu.
Wannan adadin ya fi jimillar ƴan gudun hijira na ƙasashen da ke kusa da ita wato Burkina Faso (3.58m), Nijar (2.06m), Mali (931,000) da Kamaru (1.42m) gaba ɗaya.
A cewar rahoton, Najeriya na ɗauke da kashi 44 cikin 100 na dukkanin mutanen da suka rasa matsugunnansu a yankin Yammacin Afirka.
Rahoton na UNHCR, wanda ke dogaro da bayanai daga hukumomin cikin gida da ƙungiyoyin taimako da ke aiki a ƙasashe 14 na yankin, ya bayyana cewa yawan waɗanda suka rasa matsugunsu a Najeriya bai haɗa da makiyaya da ke yawo ko masu hijira zuwa birane da ba a tantance su ba.
Tun daga shekarar 2014 bayan hare-haren Boko Haram a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, adadin IDPs ya ci gaba da ƙaruwa, inda rikice-rikicen masu satar shanu a Zamfara da Katsina, da na manoma da makiyaya a Benue da Filato suka ƙara tsananta lamarin.
WANI LABARIN: Manyan Ƴan Siyasa Bakwai Ne Ke Zawarcin Kujerar Shugaban Ƙasa Daga Ɓangaren Haɗakar ADC
Rahoton ya ce mafi yawan ƴan gudun hijirar yanzu ba sa zama a sansanonin gwamnati, suna zama cikin al’ummomin da suka karɓe su kai tsaye, lamarin da ke haifar da ƙalubale wajen isar da taimako da kuma ajiye bayanan adadinsu.
Sai dai saɓanin maƙwabtanta, Najeriya na da yawan jama’a da hanyoyin mota da suka sa ƴan gudun hijirar na iya motsawa daga wuri zuwa wuri don samun tsira.
Haka kuma, Najeriya na ba da mafaka ga kimanin ƴan gudun hijira 223,000 daga Kamaru, amma ita ma Najeriyar na da ƴan Najeriya fiye da miliyan biyu da rabi da ke zama ƴan gudun hijira ko neman mafaka a ƙasashen waje.
Hukumar NCFRMI da aka kafa tun zamanin mulkin Babangida na da alhakin kula da waɗannan mutane tare da haɗin gwiwar hukumar shige da fice ta ƙasa da UNHCR.
Amma a cewar rahoton, kuɗaɗen da Majalisar Ɗinkin Duniya da abokan hulɗarta suka nema domin tallafawa IDPs a yankin Yammacin Afirka a 2025 na dala biliyan 1.3, har zuwa Yunin da ya gabata, iya kaso 37 cikin 100 kacal aka samu, lamarin da ya sa aka rage abinci da kuma dakatar da shirye-shiryen samar da walwala ga IDPs ɗin.
Rahoton ya yi gargaɗin cewa rashin isasshen tallafi na iya kai wa ga sansanonin IDPs zama wuraren da masu tada ƙayar baya ke jan hankalin sabbin mayaƙa.