Ƴan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 3.33 A Kira Da Data A 2022

Ƴan Najeriya da sauran masu amfani da netwok a Najeriya sun kashe naira tiriliyan 3.33 a kira, saka data, tura saƙon kar ta kwana da sauran abubuwan da ake da netwok a cikin shekarar 2022, in ji Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC.

Wannan na nuni da cewar, kamfanonin sadarwa sun yi cinikin naira tiriliyan 3.33 a shekarar.

Hukumar NCC ta bayyana hakan ne a rahoton bayanan shekarar 2022 da ta fitar kan amfani da kafafen sadarwa na shekara-shekara.

Hukumar ta ce, yawan masu amfani da network a na kira ko data a Najeriya sun kai 195,463,898 a shekarar 2021 wanda a shekarar 2022 suka ƙaru har zuwa 222,571,568, abun da ya nuna ƙaruwar kaso 13.86 cikin 100.

NCC ta kuma ce, amfani da data ma ya ƙaru matuƙa a Najeriya a shekarar 2022, inda aka yi amfani da datar da yawanta ya kai TB 518,381.78 zuwa ƙarshen shekarar.

NCC
Comments (0)
Add Comment