Ƴan Sanda Sun Cafke Wani Sufeta Ɗan’uwansu Da Wasu Fararen Hula Bisa Zargin Fashi Da Makami

Rundunar ƴan sanda ta Edo ta cafke wani jami’in ƴan sanda mai aiki tare da fararen hula uku bisa zargin azabtarwa, karɓar rashawa da kuma fashi da makami da ya addabi mazauna Benin.

Kakakin rundunar, Moses Yamu ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a Benin ranar Lahadi, bayan wani bidiyo ya bazu yana nuna ƙorafin wani wanda aka ce an “sace shi, an ƙwace wayarsa da kayansa, sannan aka jikkata shi.”

Yamu ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar, Monday Agbonika, ya umarci “bin diddigi cikin gaggawa da kama dukkan masu hannu a ciki” bayan fitar bidiyon.

A cewarsa, “a ranar 15 ga Agusta 2025, tawagar sintiri ta Ugbowo ta yi nasarar daƙile mutanen da ake zargi tare da wata Toyota Yaris mai launin azurfa da wasu da ake zargi.”

Ya ƙara da cewa an kama “wani Inspector mai aiki” tare da abokan aikinsa uku fararen hula, inda CP Agbonika ya bayyana lamarin a matsayin “abin kunya, kuma babban laifi.”

Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa, “rundunar tana da zero tolerance ga cin hanci, wuce gona da iri ko aikata ba daidai ba; ba za a sami mafaka ga miyagun ɓangarori a cikin ƴan sanda ba.”

Ya kuma nanata cewa, “duk wani jami’i da aka kama da karɓar rashawa, azabtarwa ko cin hanci za a kore shi, a kama shi, sannan a gurfanar da shi,” tare da kiran jama’a, ciki har da wanda ya fito a bidiyon, “su bayar da sahihan bayanai domin a tabbatar da adalci.”

Comments (0)
Add Comment