Ƴanta’adda Sun Mayar Mu Bayi, Suna Sa Mu Aiki A Gonakinsu – Ƴan Jihar Niger

Mutanen da ke zaune a wasu garuruwa da ke fama da matsalar tsaro a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, sun koka cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga na bautar da su wajen aikin gona a gonakin su.

An gano cewar, shugaban wata ƙungiyar ƴan ta’adda ya tara fiye da buhunan wake ashirin daga gonaki a Allawa da wasu makwabtan garin a bana.

A wani taron gaggawa na manema labarai da aka yi a Minna, babban birnin Jihar Neja, Saidu Salihu, sakataren wata ƙungiyar matasa ta Shiroro, ya buƙaci a dawo da sojoji zuwa Allawa da kewaye domin mazauna su koma aikin gonakinsu.

Salihu ya bayyana cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga sun mamaye wadannan garuruwa tun bayan janye sojoji daga Allawa watanni uku da suka wuce.

Ya buƙaci gwamnatin Jihar Neja da ta ƙarfafa haɗingwiwa da hukumomin tsaro da kuma ba da kayan aiki ga matasan sa-kai domin kare garuruwan da abin ya shafa.

Har ila yau, ya buƙaci gwamnati ta ba da diyya ga mutanen da aka raba da muhallansu da dukiyoyinsu sakamakon hare-haren da suka biyo bayan janye sojojin.

Salihu ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun nemi tattaunawa da mutanen da abin ya shafa domin samun damar komawa garuruwansu amma duk da haka gwamnatoci a jiha da tarayya ba su mayar da martani ga buƙatar ba.

Abdullahi Suleiman Erena ya bayyana cewa matsalar tsaro a sassa takwas na yankin Lakpma ba ta tsaya daga ƴan bindiga ba, har da ƙungiyoyin ƴan ta’adda kamar Boko Haram, ISWAP, da Ansaru.

Ya gargaɗi cewa wannan yanayi na ƙara haifar da barazana ga yankin, wanda idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, zai iya zama da wuya a shawo kansa.

Jihar NigerMatsalar Tsaro
Comments (0)
Add Comment