Ƴan’uwan Wani Ɗalibi Da Sojoji Suka Harbe Sun Zargi Ƴansanda Da Ƙumbiya-Ƙumbiya

Ƴan’uwan Godwin Akpakpan, ɗalibin ajin ƙarshe na jami’ar Port Harcourt da aka ce sojoji sun harbe da bindiga har lahira, sun samu saɓani da ƴansanda bisa ƙin bayyana sahihin bayanin masu hannu a mutuwar sa.

Francis Akpakpan, ɗan’uwan marigayin, ya bayyana cewa Godwin ya je kallon ƙwallo ne a mashayarsa ranar 16 ga watan Afrilu kafin ya tafi gida, amma daga bisani suka kasa samun sa a waya sai wani ya ɗauka ya ce soja ne ya harbe shi.

Ya ce bayan da suka isa ofishin ƴansanda tare da lauya, an nuna musu mota da aka ce an harba, amma bayan sun ziyarci asibitin koyarwa na jami’ar, raunukan da suka gani a jikin gawarsa, waɗanda suka haɗa da harbin bindiga a ciki har sau biyu da raunuka, ba su dace da bayanin da aka ba su ba.

Yayin da suka matsa wajen neman ƙarin bayani, jami’in bincike (IPO) ya ja da baya yana cewa kada su cigaba da bincike domin “za a iya harbe su su ma.”

Francis ya ce akwai ƙarin shakku saboda wurin da aka ce an yi harbin ba shingen sojoji ba ne kamar yadda IPO ya bayyana, wanda hakan ke nuna ana yunƙurin ɓoye gaskiyar lamarin.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce an samu ƴar tsangwama tsakanin sojoji da wasu fararen hula kuma yayin da motar da Godwin ke ciki ke wucewa, harsashin soja ya same shi, kuma an kai shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa daga baya.

Kungiyar Take It Back Movement ta buƙaci a gudanar da bincike kai tsaye da gaskiya, inda shugaban kungiyar a jihar Rivers, King Amanyie, ya bayyana kisan a matsayin “cin zarafi da mummunan kalubalantar ɗan’adamtaka” tare da buƙatar a gurfanar da duk waɗanda suke da hannu a lamarin.

Comments (0)
Add Comment