Ɗalibai Ƴan Najeriya Da Rikicin Sudan Ya Koro Gida Na Roƙon Jami’o’in Najeriya Admission

Ɗalibai ƴan Najeriya waɗanda rikicin Sudan ya koro gida sun koka kan wahalhalun da suke sha wajen samun damar ci gaba da karatunsu a jami’o’in Najeriya.

In za a iya tunawa dai, ɗalibai 2,518 ne aka samu nasarar dawo da su gida Najeriya daga Sudan a watan Mayu, 2023.

A ranar 7 ga watan Yuni kuma, Hukumar Share Fagen Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ta fitar da tsarin yanda ɗalibai ƴan Najeriya da suka dawo gida daga ƙasashen da ke fama da rikici, ciki har da Sudan, zasu sami damar shiga manyan makarantun Najeriya.

Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede ya ce, tsarin gaggawa na neman canjin wajen karatu (transfer) ga ɗalibai na buƙatarsu da su sabunta rijistarsu da Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa.

Ɗalibai da dama da suka sami zantawa da wakilin PUNCH sun bayyana cewa, har kawo wannan lokaci ba su sami damar shiga jami’o’in Najeriyar ba saboda tsaurin da ke cikin hanyoyin da zasu bi.

Wani ɗalibi, kuma Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Jigawa da ke Sudan, Umar Abubakar, ya yi ƙorafin cewa, mafi yawancin takardunsa har yanzu suna can Sudan, inda ya ƙara da cewa, samun tantancewa daga Ma’aikatar Ilimi yana da matuƙar wahala.

Umar ya ce, “Har yanzu ban sami admission ba. Akwai buƙatar sai na bi tsare-tsaren da JAMB ta gindaya. Sai na je Abuja daga Kano. Kuma mafi yawanmu sun baro takardunsu a Sudan.

“Ba zamu iya samun takardun shaidar karatunmu daga jami’o’in Sudan ba a yanzu saboda rikici. Ina iya bakin ƙoƙari na don ganin na sami takardu na, musamman sakamakon WAEC da kuma amincewar Ma’aikatar Ilimi sannan na ɗora su a shafin yanar gizo na JAMB.

“A Jami’ar Bayero da ke Kano nake so na yi karatu, saboda suna da Sashin Koyar da Ilimin Harhaɗa Magunguna (pharmacy). Hanyar da mutum zai bi ya sami takardunsa ko amincewar Ma’aikatar Ilimi ta yi matuƙar wahala saboda yawan ɗaliban da suka dawo daga Sudan.”

Haka shi ma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Katsina da ke Sudan, Isma’il Abubakar ya ce, har yanzu bai sami damar shiga Jami’ar Bayero da ke Kanon ba, bayan kuma ya kammala shigar da dukkan takardunsa a safin JAMB.

Isma’il ya bayyana cewa, “Har yanzu ba a ɗauke ni ba. Na tura buƙatar a ba ni gurbin karatu a Jami’ar Bayero bayan JAMB ta tantance ni amma har yanzu babu wani abu daga garesu. Yanzu haka abin na damuna.”

Ita ma wata ɗalibar Karatun Likitanci a Jami’ar Hayat da ke Sudan, Amira Tafida ta ce, makarantar da ta zaɓa har yanzu ba su kira ta tantancewa domin ba ta admission ba.

Amira ta ce, “Na nemi shiga Eko University of Medical and Health Sciences, da ke Jihar Lagos, amma har yanzu ba su ɗauke ni ba. Da ina tunanin ko Jami’ar Abuja ko kuma Jami’ar Eko, amma daga baya na yanke kawai zan je Jami’ar Koyon Aikin Likitancin, saboda ta fi kusa da ni, tun da a Lagos nake zaune.

“Zasu yi min gwaji domin sanin irin ilimin da na samu game da fannin, abin da zai ba su damar gane ajin da ya kamata su saka ni, duk da dai har yanzu makarantar ba ta sa lokacin yin wannan gwajin ba.”

Haka shi ma, ɗalibi ɗan aji uku a karatun Ilimin Fasahar Sadarwa, ICT, Abdulsalam Maikano ya ce, “Har yanzu ban sami admission ba a kowacce daga jami’o’in Najeriya.

“Yanzu ina kan bin tsarin da JAMB ta bayar ne, duk da dai ban fara a kan lokaci ba, saboda ban daɗe da sanin tsarin ba. Ina shirin zaɓar Jami’ar Al-Qalam da ke Jihar Katsina ko kuman Jami’ar Skyline da ke Jihar Kano.

Ita kuma ɗalibar ajin ƙarshe a fannin haɗa magunguna (pharmacy), a Jami’ar Ƙasa da Ƙasa ta Sudan, Zainab Mohammed, ta bayyana cewa, yanzu haka tana ci gaba da karatunta ta hanyar yanar gizo a makarantarta ta Sudan kafin kuma abin da zai biyo baya.

Gurbin KaratuJAMBRikicin Sudan
Comments (0)
Add Comment