Ɗan Majalissar Jigawa Mai Wakiltar Birnin Kudu Zai Nemawa Matasa Guraben Karatu

Ɗan Majalissar Jihar Jigawa mai wakilatar Mazaɓar Birnin Kudu, Muhammad Kabir Ibrahim ya yi alƙawarin nemawa matasan mazaɓarsa guraben karatu a Kwalejin Horar da Malamai ta Jihar Jigawa da ke Gumel.

Ɗan Majalissar ya bayyana hakan ne a sanarwar da mai taimaka masa, Ibrahim Rabi’u Birnin Kudu ya aikowa TASKAR YANCI a yau.

Ibrahim ya bayyana cewa, ɗan majalissar ya yanke shawarar yin hakan ne domin temakawa matasa mata da maza na mazaɓarsa wajen samun sauƙin bunƙasa harkokin iliminsu.

Ya ƙara da cewa, tsare-tsare sun yi nisa kan yanda za a gudanar da aikin neman guraben karatun cikin nasara.

Ibrahim ya kuma ce an fitar da ƙa’idojin da masu son morar shirin zasu cika kafin su mora, waɗanda suka haɗa da samun shaidar gwamnati ta kasancewa ɗa ko ƴar asalin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu.

Labari Mai Alaƙa: Gwamnatin Kano Zata Bayar Da Tallafin Karatu Ga Masu 1ST Class A Jihar

Sauran ƙa’idojin sun haɗa da mallakar credits biyar a jarabawar kammala sikandire waɗanda suka haɗa da Turanci da kuma Lissafi.

Akwai kuma sharaɗin cin jarabawar JAMB ta shekarar 2023 da makin da ya kai 100 zuwa sama, da kuma kasancewa mai sha’awar samun horon karatun aikin koyarwa na NCE a Gumel.

Sanarwar ta buƙaci duk wanda ya cika waɗannan ƙa’idoji da ya kai kwafi na takardunsa ofishin ɗan majalissar da ke shagunan bayan gidan sarki.

Kwafin takardun da za a kai sun haɗa da Jamb Result, SSCE Result, Primary Certificate, Declaration of Age/Birth Certificate, Indigene Certificate, Passport Photograph da lambar waya da kuma email masu yi.

Za a karɓi takardun ne a tsakanin ranar Talata 1 ga watan Agusta zuwa Lahadi 20 ga watan Agusta, 2023, sannan kuma masu sha’war shiga shirin zasu iya tuntuɓar waɗannan lambobi: 07038981998 da kuma 07067500700.

Birnin KuduGurbin KaratuMuhammad Kabir Ibrahim
Comments (0)
Add Comment