Ɗan Takara Daga Arewa Ne Kadai Zai Iya Kayar Da Tinubu A 2027, In Ji Wani Lauya Ɗan Kudu

Mai goyon bayan haɗaka kuma lauya Kenneth Okonkwo ya bayyana cewa tilas ne jam’iyyun adawa su tsayar da ɗan takara daga yankin Arewa idan har suna da niyyar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A hirar da ya yi a shirin Politics Today na Channels TV, Okonkwo ya bayyana cewa “dole ne mu tallafa wa ɗan Arewa domin idan ka tsayar da ɗan kudu, Tinubu zai ci zaɓe kai tsaye.”

Ya ƙara da cewa “idan Arewa na goyon bayan Atiku, Tambuwal ko El-Rufai, ya kamata su tsaya takara,” yana mai jaddada cewa ɗan takarar, dole ne ya kasance da gogewa da karɓuwa a faɗin yankin.

Okonkwo, wanda a baya yana daga cikin masu magana da yawun Peter Obi a jam’iyyar Labour, ya bar jam’iyyar a watan Yuli 2024 sakamakon rikicin cikin gida da rashin iya warware matsalolin jam’iyyar.

WANI LABARIN: Dangote Ya Sake Rage Farashin Fetur Da Ake Sarowa Daga Matatarsa

Ya ce “duk wanda ya kawo ɗan kudu don ya fafata da Tinubu yana sauƙaƙa masa hanya ne, saboda babu wani shugaban ƙasa daga kudu da ya taɓa ƙalubalantar shugaban ƙasa mai ci daga kudu.”

A cewarsa, “idan Obi ya sake tsaya wa, za a ƙwace masa nasara kamar yadda aka yi a 2023, saboda babu wata kafa mai ƙarfi da ke goyon bayansa.”

Okonkwo ya jaddada cewa hanya mafi tasiri ita ce tsayar da ɗan Arewa mai ƙarfi da za a iya haɗawa da wani mataimaki daga kudu domin tabbatar da nasara.

A ranar 2 ga Yuli, 2025, shugabannin adawa ciki har da Atiku, Obi, El-Rufai, David Mark da Aregbesola sun bayyana jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za su yi amfani da shi wajen ƙalubalantar APC a 2027.

A zaɓen 2023, Atiku da Obi sun tara sama da ƙuri’u miliyan 12 idan an haɗesu, wanda ya fi adadin ƙuri’un da INEC ta bayyana cewa Tinubu ya samu.

Okonkwo ya ce lokaci ya yi da za a tsara dabarun siyasa bisa gaskiya da amfani da ƙarfi daga Arewa domin yin nasara.

Comments (0)
Add Comment