Ƙungiyar nan ta ƙasa-ƙasa da ke aiyukan ƙarfafar ci gaban harkokin lafiya, na neman ma’aikatan da zata tura domin tattara bayanai da lura da al’amuran aiyukanta, Field Officers, a jihohin Jigawa, Katsina da kuma Zamfara.
Field Officers ɗin zasu yi aiki ne wajen ƙarfafar shirin New Incentives na tura kuɗaɗe domin ƙarfafar iyaye mata wajen ganin sun kammala aikin samarwa jariransu rigakafin da ake buƙata.
Babban aikin waɗanda za a ɗauka shine shigar da bayanan iyayen a asibitocin gwamnati na jihohin guda uku.
Dole ne mai neman aikin daga Jihar Jigawa ya kasance mazaunin waɗannan garuruwa: Gwiwa. Gumel, Yankwashi, Kazaure, Miga, Maigatari, Kiyawa, Gwaram, Dutse, Buji, Kafin Hausa, Malam Madori, Auyo, Sule Tankarkar, Gagarawa, Roni, Babura, Jahun, Kaugama, Kiri Kasama, Guri, Garki, Hadejia, Taura, Birnin Kudu, Biriniwa da kuma Ringim.
Dole ne mai neman aikin daga Jihar Katsina ya kasance mazaunin waɗannan garuruwa: Musawa, Zango, Dan Musa, Sandamu, Matazu, Mashi, Katsina, Sabuwa, Kaita, Dutsi, Dandume, Batsari, Jibia, Danja, Batagarawa, Rimi, Kankara, Malumfashi, Kafur, Mani, Funtua, Kusada, Bindawa, Daura, Mai’Adua, Baure, Faskari, Dutsin Ma, Bakori, Kurfi, Charanchi, Kankia, Ingawa da kuma Safana.
Dole ne mai neman aikin daga Jihar Zamfara ya kasance mazaunin waɗannan garuruwa: Bungudu, Birnin Magaji-Kiyaw, Gusau, Talata, Mafara, Zurmi, Kaura Namoda, Anka, Maru, Tsafe, Shinkafi, Bakura, Gummi, Maradun da kuma Bukkuyum.
Ana buƙatar mai neman aikin ya kasance yana da takardar shaidar kammala diploma ko degree musamman a ɓangaren ilimin harkar lafiya, sannan kuma ana son ya kasance wanda ya iya yaren da ake yi a garuruwan da zai nemi aikin.
Za a baiwa mata muhimmanci matuƙa a ɗaukar aikin sama da maza.
A lokacin neman mai neman zai ɗora hoton takardar CV nasa mai shafi ɗaya da kuma wasiƙar nuna sha’awar aikin da ba ta haura kalmomi 300 ba.
Za a nemi aikin ne kaɗai ta shafin Breezy HR da aka ware, ana gargaɗin masu nema da kar su nema ta wata hanyar ba wannan ba.
Ga mai sha’awar nema zai shiga wannan shafi domin neman ƙarin bayani da kuma cikewa: https://new-incentives.breezy.hr/p/1b0a4d9ed51a-1-field-officers-entry-level