A Yau Alhamis Tinubu Zai Lula Ƙasashen Waje Don Gudanar Da Wasu Ayyukan Gwamnatinsa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai fara ziyarar ƙasashen Japan da Brazil daga ranar Alhamis, tare da tsayawa kaɗan a Dubai, UAE, domin halartar taron TICAD9 a Yokohama, Japan daga 20 zuwa 22 ga Agusta.

An shirya taron ne da taken “Co-create Innovative Solutions with Africa” domin bunƙasa tattalin arziƙin Afirka ta hanyar zuba jari da ƙirƙire-ƙirƙire.

Bayan Japan, Tinubu zai wuce Brazil daga 24 zuwa 25 ga Agusta domin ganawa da shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da kuma shiga taron kasuwanci da masu zuba jari.

Za a tattauna kan yadda ƙasashen biyu za su ƙara haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, ciki har da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi.

Tinubu zai haɗu da manyan kamfanoni da nemo zuba jari a Najeriya domin inganta yanayin kasuwanci.

Taron TICAD an fara shi ne a 1993 tare da haɗin gwiwar UN, UNDP, AU, da World Bank, kuma ana gudanar da shi sau ɗaya cikin shekara uku, a madadin Japan da Afirka.

An gudanar da taron na ƙarshe a Tunisia a 2022.

Tinubu zai jagoranci tawagar ministoci da manyan jami’ai a ziyarar.

Wannan ziyarar na nufin ƙara bunƙasa hulɗar kasuwanci da zuba jari tsakanin Najeriya da ƙasashen duniya.

Comments (0)
Add Comment