Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi hukumar EFCC da yin bincike bisa son rai da kuma zama tamkar rundunar farautar abokan hamayya ga jam’iyyar APC mai mulki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, ADC ta bayyana cewa dabarun hukumar na baya-bayan nan na buɗe shari’o’in da aka rufe shekaru da dama da suka wuce, tare da tuhumar manyan ƴan adawar ƙasar, ya nuna cewa ba ta aiki a matsayin hukumar yaƙi da cin hanci mai zaman kanta.
“Waɗannan ba sabbin shari’o’i bane da suka fito daga sabbin hujjoji, amma an buɗe su ne a matsayin martani ga sabuwar dangantakar siyasa don tsoratar da manyan ƴan adawa,” in ji sanarwar.
ADC ta ce EFCC an ƙirƙire ta ne don ta zama “mai tsaron amincin jama’a” wadda za ta yi amfani da doka ba tare da nuna bambanci ba, amma a yau wannan manufar ta lalace.
“Hukumar yanzu na aiki kamar wani sashen APC, ana tura ta domin ta kai hari kan masu suka da ƴan adawa,” in ji jam’iyyar.
Sanarwar ta nuna cewa ana barin binciken da ya shafi abokan gwamnati ya shuɗe ba tare da wani ci gaba ba, amma ana tsananta wa ƴan adawa da tsoffin tuhume-tuhume na shekaru da dama da aka ɗauko a matsayin sabbi.
“Wannan shi ake kira bincike bisa son rai, kuma bincike bisa son rai shi ne kashe adalci,” in ji Abdullahi.
Ya ƙara da cewa a yau a Najeriya laifi ko rashin laifi ya dogara ne da jam’iyyar da mutum ya shiga, ba da hujja ba.
Misali, ya ce, wani tsohon gwamna tun da ya koma APC tare da cikakken tsarin siyasar jiharsa, duk binciken EFCC game da gwamnatinsa ya ɓace babu wani rahoto ko sabuntawa.
ADC ta ce wannan hali ya haifar da ra’ayi mai hatsarin cewa “abinda kawai za ka yi don ka ja hankalin EFCC shi ne ka tsaya adawa da mai mulki, kuma kariya ita ce ka koma bayan gwamnati.”
Jam’iyyar ta yi kira ga ƴan Najeriya, ƙungiyoyin fararen hula, da kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da su hana wannan karkacewa zuwa mulkin kama-karya da amfani da hukumomin jama’a don cimma burin siyasa.
“EFCC ba ta APC bace, mallakar al’ummar Najeriya ce,” in ji sanarwar.