Aikin Gina Hadejia Specialist Hospital Na Daya Daga Cikin Manyan Aiyuka Masu Kalubale Da Danmodi Ya Gada A Jigawa

Daga: Ahmed Ilallah

Wannan aikin gina Asibitin Wanda a ka soma tun 2017, bisa alkawarin kammali a kasa da shekara biyu, sai ga shi yay shekara kusan bakwai kenan har yanzu ba a kai ga kammalawa ba.

Tabbas mutanen yankin da basu da wata babbar Asibitin a yankin, in har jinyar da ta  wuce General Hospital to dole sai sun dangana da a kalla Nguru, Kano ko Dutse, su nuna damuwa da kin karasa wannan aiki.

Shi wannan aiki tun farkon fara shi a 2017 ya sha fama da kalubale kala-kala, wanda ya kawo wa aikin cikas.

Kamar yadda na fada ina tausayin Maigirma Gwamna a kan wannan aiyukan, wannan Asibitin, matsalar Hadakar Fansho da karancin ma’aikata a bangaren ilimi da lafiya da sauran ma’aikatun gwamanatin.

Ga abin da yakamata mutane su fahimci game da kalubalen da wannan aiki ya fuskan ta.

Matsalar Hadejia Specialist

An kandamar da aikin ginin Asibitin mai gado 250 a ranar 27/12/2017, wanda Gwamna Badaru yayi alkawarin kammalawa a wata goma 18. An bada kwangilar a kan kudi N1.5B, wanda a ka kara ya zama N1.8B ga kamfanin PHILKO CONSTRUCTION COMPANY.

Zan so duk dan kishin kasa yayi binciken su waye masu kamfanin PHILKO da a ka bawa wannan kwangila? Domin a kwai abubuwa da dama da suka faru a baya, da muke gwagwarmaya a kan wannan aiki, har ya kusa kai ….. gaban KULIYA.

Yadda Gwamnatin A Baya  Ta Ke Sa Kudi A Kan Aikin Asibitin

Bayan kaddamar da aikin da Gwmana Badaru yayi da alkawarin kamala shi a watanni 18, ga maganar sa da turanci a wurin kaddamar da aikin “This hospital will be built in 18 months and will be commissioned in 2019,”.

A kasafin kudin shekara 2017, an sanya N1.2B don aiyukan Asibitocin General Hospital, Birnin Kudu cigaba, Hadejia Specialist Hospital farawa, da Kazaure Specialist Hospital farawa, amma fa abin gwamnatin ta iya sanya wa a wannan aiyuka shine N377 milyan.

A  kasafin kudin 2018, an amince da kashe N600, a kan wannan asibitoci, amma abin da a ka kashe a wannan shekarar shine N 746 million, sama da abin da kasafin kudi ya tanada.

A kasafin kudin 2019 an amince da kasha N1.5 billion a kan wannan asibitoci, amma abin da aka kasha shine N1.4 billion. Nawa a ka kashe a Hadejia?

A 2020, a bin da aka ware shine N1.6 billion, amma N795 million kacal a ka kashe a aikin asibitocin.

A shekara 2021 a ware N3.3 billion don aikin Asibitocin. Shin nawa a kashe a Hadejia?

Bayan wannan kididdiga ta sama ya kamata mu sake sani cewa akwai cece-kuce a kan kamfanin farkon da aka bawa kwangilar ginan Asibitin.

A ranar 2/12/2022, Gwamnatin Jahar Jigawa ta soke kwangilar da ta bawa kamfanin PHILKO ta bawa kamfanin Kahadhir Global.

Shin in zamu yi adalci, a ina wannan matsalar take?

Ni a ra’ayina wannan gwamnati ta gaji wannan aiyuka ne, wanda suke da matsaloli daban daban.

Ahmed Ilallah ya rubuto ne daga Hadejia, Jihar Jigawa

Comments (0)
Add Comment