AJAERO: Babu Wanda Ya Fi Ƙarfin Doka, In Ji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa babu wanda ya wuce doka, ciki har da shugaban NLC, Joe Ajaero, bayan zarginsa da kin amsa gayyatar hukumomin tsaro.

An kama Ajaero ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, yayin da yake shirin tafiya taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Biritaniya, TUC a Landan.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya ce Ajaero ya ki amsa gayyatar hukumar DSS da ke binciken sa.

Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, babu wanda ke da ikon bijirewa gayyatar hukumomin tsaro ko bincike na doka.

Ajaero dai ya bayyana cewa an saki fasfonsa da wayoyin sa da DSS ta karɓe, bayan kamun da aka yi masa.

DSS ta kuma ce ziyarar da jami’anta suka kai ofishin SERAP ba mamaya ba ce, illa kawai bincike suke yi.

Sai dai shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki kama Ajaero da kuma mamaye ofishin SERAP.

A yanzu dai an samu labarin cewa DSS ta janye jami’anta daga ofishin SERAP da suka yi wa kwanton bauna a baya.

Onanuga ya kara da cewa babu wanda zai ki amsa gayyatar hukumomin tsaro a kasashen Biritaniya ko Amurka ba tare da ya fuskanci hukunci ba.

Ya kuma ce gwamnatin Najeriya ba ta take hakkin dan adam ba kamar yadda kungiyar TUC ta Biritaniya ta zargi.

Ya jaddada cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da kare ƴancin dukkan ƴan Najeriya tare da tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasa.

DSSNLC
Comments (0)
Add Comment