Akwai Wike, El-Rufai, Edun, Oyetola, Adelabu Da Sauransu A Sunayen Ministocin Tinubu

A yau ne sunayen waɗanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke san naɗawa a matsayin ministoci zai bayyana a Majalissar Dattawa domin tantancewa.

Wasu sanannu da aka gano sunayensu a jerin sunayen ministocin sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sadarwa da Tsare-tsare, Dele Alake, tsohon Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola, Wale Edun, tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, Adebayo Adelabu da kuma Beta Edu.

Adelabu dai tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ne, yayin da Beta Edu ta taɓa riƙe Kwamishiniyar Lafiya a Jihar Cross River sannan a yanzu kuma take a matsayin Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC ta Ƙasa.

Labari Mai Alaƙa: Rikicin APC Ya Ƙara Ƙamari, Mataimakin Shugaban Jam’iyya Ma Ya Ajjiye Aiki, Ya Zargi Tinubu

An dai ta yaɗa jerin sunayen ƙarya na ministocin, yayin da Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ƙyale ƴan Najeriya suna ta hasashe.

Bayanai dai suna cewa, tsoffin gwamnoni, ƙwararru da masana ne suka samu kasancewa a ministocin na Tinubu.

An kuma gano cewa, domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, Shugaban Ƙasar ya saka sunayen wasu manyan mutanen da suka fito daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

An gano cewa, Tinubu ya ware sunayen mutane 43 ne a matsayin ministocin, yayinda kowacce jiha da Abuja suka sami minista ɗai-ɗai, sai kuma ministoci shida da suka fito daga yankuna shida na Najeriya.

Akwai yiwuwar ƙwararren lauyan nan Lateef Fagbemi, SAN ne zai kasance Ministan Shari’a a gwamnatin ta Tinubu.

Bola Ahmed TinubuMajalissar DattawaSunayen Ministoci
Comments (0)
Add Comment