Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa wahalar tattalin arziki da Najeriya ke ciki ba daga Allah take ba, yana mai nuni da arzikin kasa da Allah Ya albarkaci Najeriya da shi.
Obasanjo ya yi wannan bayani ne yayin bikin cika shekaru 40 na Archdiocese na Cocin Methodist ta Abuja, wanda aka gudanar a babban birnin tarayya.
Yayin da yake Magana kan albarkatun Najeriya, ya yi kira ga shugabannin kasar da su yi amfani da wadannan arzuka wajen bunkasa kasa.
Ya ce, “Najeriya tana da dukkan abin da take bukata domin ta samu ci gaba,” yana mai goyon bayan jawabin shugaban Cocin Methodist, Dr. Oliver Aba, wanda ya jaddada muhimmancin gode wa Allah.
Obasanjo ya bayyana cewa “kamar yanda Allah ya albarkaci kasar Masar da Kogin Nilu, haka ya albarkaci Najeriya da kogunan Neja da Benue, man fetur, da kuma ƙasa mai albarka.”
Ya kara da cewa, “Ina da yakinin cewa Allah bai halicci Najeriya don ta wahala ba. Mun ɓata albarkatun da Allah ya ba mu, amma idan muka koma ga Allah, zai warkar da kasarmu.”
A karshe, ya jaddada bukatar shugabanni da su nemi zaman lafiya da hadin kai wajen magance kalubalen kasa.