Ambaliya Ta Cinye Gandun Sarki A Haɗejia, Gidaje Da Dama Sun Rushe Yayin Da “Kamfanin Aikin Titi Ya Toshe Magudanan Ruwa”

Daga: Lukman Dahiru

Ruwan sama mai yawa wanda ya ɗauki sama da sa’o’i 15 ya yi mummunar ɓarna a unguwar Gandun Sarki ta ƙaramar hukumar Malammadori da ke garin Haɗejia, inda sama da gidaje 40 suka rushe, yayin da sassan gidaje fiye da 100 suka lalace.

Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan matsala daɗaɗɗiya ce da ke ƙara ta’azzara duk lokacin damuna saboda toshewar magudanan ruwa da rashin tsari.

Basaraken gargajiya a yankin, Mallam Musa Musa, ya ce, “Ƙarancin magudanan ruwa da toshewar waɗanda ake dasu na daga cikin manyan barazanar da muke fama da su.”

Ya danganta lamarin da aikin wani kamfanin tituna mai suna Cosgrove, wanda ya ce “ya yi aikin da bai dace ba, ya toshe magudanan ruwa, kuma hakan ya jefa mu cikin masifa.”

Ya bayyana cewa, “Kwana biyar da suka gabata gwamnatin jiha ta turo jami’an gwamnati domin ganin halin da ake ciki, kuma an yi alƙawarin ɗaukar mataki,” sai dai har yanzu shiru.

Duk da haka, ya gargaɗi cewa, “Babu yadda za mu samu nasara idan wannan kamfanin bai dawo ya yi aikin da ya dace ba.”

Basaraken ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin dindindin wajen gyara magudanan ruwa domin kare ɗaruruwan iyalai daga matsalar da ta zama tamkar ƙaddara a kowace damuna.

Comments (0)
Add Comment