Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Birnin Yenagoa Na Jihar Bayelsa

Mamakon ruwan sama da aka yi daga ranar Talata zuwa Laraba ya jawo ambaliyar ruwa a yankuna da dama na Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Yankunan da suka fi shan wahala sun haɗa da maƙabarta, Azikoro, Ekeki, Okaka, Swali, Kpansia, Amarata da Ovom.

Ruwan saman ya ƙara haddasa tashin ruwan Kogin Epie da Kogin Nun, wanda ya nuna yiwuwar ambaliyar ruwa mai tsanani kafin wannan lokacin.

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan haɗarin da ke tattare da ƙaruwar ruwan, yayin da hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa da haɗari a wasu jihohi daga jiya Laraba zuwa gobe Juma’a.

A Jihar Bayelsa, da ke kusa da teku, rashin tsari mai kyau na gine-gine da rashin magudanan ruwa isassu sun ƙara dagula yanayin.

A yankuna kamar Amarata da Ekeki, mazauna sun riƙa amfani da kwanduna da bokitai don yashe ruwa daga gidajensu, wasu kuwa kadarorinsu da dama sun lalace.

Wani masanin muhalli, Alagoa Morris, ya bayyana cewa ambaliyar ta cinye gidansa da ofisoshinsa.

Wani mazaunin Amarata, Nathan, ya ce ya dawo daga aiki ranar Talata ya tarar matarsa da ɗansa suna ta kwashe ruwan daga gidansu.

Ambaliyar RuwaJihar Bayelsa
Comments (0)
Add Comment