Ambaliyar ruwa mai tsanani ta shafi jihohi 29 na ƙasar nan, inda adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 192, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).
Ambaliyar, wadda aka alaƙanta da samun yawaitar ruwan sama da kuma ƙaruwar ruwa a cikin kogin Niger da Benue, ta shafi al’ummomi a faɗin kasa nan, inda sabbin rahotanni suka nuna karuwar mutuwar mutane daga Jihar Filato.
Mai magana da yawun NEMA, Ezekiel Manzo, ya jaddada cewa duk da gargadi da wayar da kan jama’a da aka yi, mutane da yawa sun yi watsi da barazanar ambaliyar, wanda hakan ya haifar da yawan mutuwar mutane fiye da yadda aka zata.
Manzo ya kuma bayyana cewa girman ambaliyar ya zarce yanda a kai hasashe a wasu yankunan, sannan an samu wasu yankunan da suka fuskanci ambaliya a karon farko a tarihi.
Hukumar tana cigaba da gudanar da aikin wayar da kan jama’a don rage hadurran ambaliyar yayin da daminar bana ke ci gaba da ƙarewa.
Kokarin na NEMA dai na da muhimmanci wajen magance wannan bala’in da kuma ba da tallafi ga al’ummomin da abin ya shafa.