An Ƙara Kama Emefiele Kan Zargin Ta’addanci

An ƙara kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele a ranar Talata bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan ashirin.

Jami’an Tsaro na Farin Kaya, DSS, ne suka kama shi bayan sun yi artabu da jami’an Kula da Gyaran Hali kan wanda ya kamata ya ci gaba da riƙe dakataccen gwamnan bankin.

Emefiele, wanda aka gurfanar da shi a kotun a jiyan da misalin ƙarfe 9:21 na safe gaban Alƙali Nicholas Oweibo kan zarge-zarge guda biyu na mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba, ya bayyana cewa shi bai aikata laifi ba.

A Karanta Wannan: Gwamnatin Jigawa Na Neman EFCC Ta Ƙwato Mata Kadarorinta A Kano

Wannan ta sa Babbar Kotun Tarayyar ta bayar da belinsa kan ya gabatar da kuɗi naira miliyan ashirin da kuma kadara mai makamancin wannan kuɗin.

Bayan bayar da belin ne kuma kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, inda kotun ta miƙa Emefiele ga jami’an kula da Gidan Gyaran Hali domin su ajjiye shi kafin ya kammala cika ƙa’idojin belinsa.

To amma bayan yunƙuri na jami’an gidan gyaran hali na cika umarnin kotu, jami’an DSS suka zo suka fi ƙarfinsu inda suka ƙara tafiya da Emefiele bisa zarginsa da aikata ta’addanci.

Wata majia da take bibiyar tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefiele ce ta ce, DSS sun ƙara kama shi ne bisa la’akari da umarnin a kama shi da wata kotun majistare ta bayar.

DSSGodwin Emefiele
Comments (0)
Add Comment