An Buƙaci Tinubu Ya Zama Mai Shigar Da Ƙara A Kotun Duniya Kan Isra’ila, An Ce Lokaci Ya Yi

Ƙungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta shiga ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar a Kotun Duniya ICJ kan Isra’ila.

Shugaban MPAC, Disu Kamor, ya ce abin ya zama dole ganin yadda duniya ke kallo kawai da nuna tsoro.

Ya bayyana cewa “waɗannan ayyuka suna ɗauke da alamun kisan ƙare dangi, manyan laifukan yaƙi, da laifukan musgunawa bil’adama.”

Ya gode wa Afirka ta Kudu kan “jarumtaka da tsarkin zuciya” wajen amfani da Yarjejeniyar Kisan Ƙare Dangi wadda Najeriya ma ta amince da ita.

“Lokaci ne na nuna gaskiya ga al’umma, Najeriya bai kamata ta iya yin shiru ko nuna halin ko-in-kula ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “tarihi ba zai yi wa ƙasashen da suka zaɓi yin shiru adalci ba, don haka mu tsaya tare da masu neman adalci.”

MPAC ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga ƙarar a matsayin mai shigar da ƙara, tare da ɗaukar matsayi mai ƙarfi a Majalissar Ɗinkin Duniya domin “a dakatar da kashe-kashen Falasdinawa nan take.”

Comments (0)
Add Comment