An Cimma Matsaya Da Gwamnati, Gobe NNPC Zai Fara Sayar Da Man Dangote

Gwamnatin Tarayya da Matatar Dangote sun cimma yarjejeniya kan samar da man fetur, inda jigilar man daga matatar zata fara gobe Litinin.

Kamfanin Mai na Najeriya, NNPC, zai kasance shi kadai ne mai ɗaukar man fetur daga matatar ta Dangote, yayin da sauran ƴan kasuwa zasu saya daga kamfanin.

Malam Zacch Adedeji, shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya, FIRS, kuma mamba na kwamitin tallata harkokin man fetur, ya bayyana cewa, NNPC zai fara kai ganga 385,000 ta ɗanyen mai ga Matatar Dangote daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Yarjejeniyar ta tabbatar da cewa Matatar Dangote zata samar da fetur da dizal a kasuwar cikin gida, wanda za a na biyanta a Naira.

Matatar Dangote zata na sayar da dizal ga duk mai sha’awa a Najeriya ba tare da sa hannun NNPC ba, yayin da iya NNPCn ne kaɗai zai sayi fetur daga matatar domin rarrabawa ƴankasuwa.

Ana dai ganin cewa, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen magance ƙarancin man fetur a kasa baki daya, tare da bayar da damar cigaba da biyan tallafin man fetur.

Matatar DangoteNNPCL
Comments (0)
Add Comment