An Dakatar Da Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya

Majalissar Zartarwa ta Kasa, NEC, ta dakatar da shirin janye tallafin man fetur wanda a baya aka tsara cirewa a watan Yunin bana bayan karewar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Da take yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala zaman Majalissar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmed ta ce, Majalissar Zartarwar ta Kasa ta amince da cewa wannan lokacin bai dace da cire tallafin man ba.

Ta kara da cewa, akwai bukatar ci gaba da tuntuba da kuma tattaunawa kan cire tallafin, da kuma fitar da ingantaccen tsari da ma yin aiki tare da gwamnoni da wakilan sabuwar gwamnati mai zuwa.

A dai watan Oktoban bara ne, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa, a shekarar 2023 tallafin mai zai zo karshe, inda ya ce abu ne da ba zai ci gaba ba a yanayin matsalar kudaden da ake ciki.

A lokacin da yake gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin 2023 ga Majalissar Tarayya ta Kasa, Shugaban Kasar ya ce, cire tallafin ya zama dole ga kasa domin tattala karamin tattalin arzikinta tun da akwai hanyoyin da za a bi wajen magance radadin cire tallafin.

Shugaba Muhammadu BuhariTallafin Man Fetur
Comments (0)
Add Comment