An Gano Fiye Da Naira Biliyan 80 A Asusun Wani Shugaban NNPC

Hukumar EFCC ta kama tsoffin shugabannin kamfanonin gyaran matatun mai na Port Harcourt, Warri da Kaduna tare da wasu manyan jami’an kamfanonin saboda zargin almundahana ta fiye da dala biliyan 2.9 da aka ware don gyaran matatun, yayin da rahotanni ke nuna cewa an gano fiye da naira biliyan 80 a asusun ɗaya daga cikinsu.

Jami’in EFCC ya bayyana cewa “muna binciken yadda aka kashe kuɗaɗen da aka fitar kwanan nan domin gyaran matatun, kuma dukkanin waɗanda suka shugabanci matatun a wancan lokacin muna gayyatarsu, wasu mun riga mun kama su.”

A cewar bayanan, dala biliyan 1.5 aka ware wa matatar Port Harcourt, dala miliyan 740.6 aka ware wa matatar Kaduna, yayin da matatar Warri ta samu dala miliyan 656.9; amma duk da haka, matatun sun gaza dawowa aiki yadda ya kamata, har ma aka sake rufe ta Warri bayan wata ɗaya da fara aiki.

“Ina matuƙar baƙin ciki,” in ji wani babban jami’in NNPCL da ya buƙaci a sakaya sunansa, “saboda duk wanda ke da hannu yana fuskantar bincike yanzu haka, ciki har da tsohon shugaban NNPCL Mele Kyari.”

Rahotanni daga jaridar Saturday PUNCH sun ce wani daga cikin tsoffin shugabannin yana hannun EFCC tun makonni da suka wuce, kuma ana ci gaba da binciken wasu masu ruwa da tsaki ciki har da Bala Wunti da sauran tsoffin manyan jami’an kamfanin.

WANI LABARIN: Tinubu Ya Sa Ranar Da Za A Kammala Aikin Layin Dogo Na Kano-Jigawa-Katsina-Maradi

Duk da tallatawar da aka yi cewa Port Harcourt da Warri sun dawoTinubu Ya Sa Ranar Da Za A Kammala Aikin Layin Dogo Na Kano-Jigawa-Katsina-Maradi aiki a watan Nuwamba da Disambar 2024, rahotanni na kwanan nan sun tabbatar da cewa matatar Port Harcourt ba ta aikin da ya kai kashi 40 cikin 100, yayin da aka rufe matatar Warri tun ranar 25 ga Janairu 2025 saboda matsalar injin dumama mai.

“Haka kawai gwamnati ke yaudarar jama’a,” in ji masanin makamashi, Kelvin Emmanuel, a wata hira da Arise TV, yana mai cewa gyaran matatun ba gaskiya ba ne, illa kawai yaudarar jama’a.

Ya ce kuɗin da aka ware tun 2021 ya isa a gina sabuwar matatar mai mai fitar da ganga 60,000 a rana, amma “ba a ga wani abu na a-zo-a-gani ba.”

Rahoton ya ƙara da cewa kamfanin ya yi iƙirarin cewa matatar Warri da ta Port Harcourt na aiki, alhali man fetur da ke kasuwa na fitowa ne daga Legas, ba daga matatun ba.

Binciken ya kuma tabbatar da cewa Warri ba ta fitar da man fetur ba tun bayan da aka sake rufe ta, kuma ba a ga motocin ɗaukar mai suna shiga ko fita daga matatar ba.

“Hukumar ba ta faɗin gaskiya ga al’umma,” in ji wani jami’i; yayin da ma’aikatan wucingadi a matatar Warri suka yi barazanar shiga yajin aikin da ka iya hana sake fara ayyukan wani sashe na matatar a ranar Litinin mai zuwa, bisa zargin rashin biyan haƙƙoƙi da cin zarafin da ake musu a wurin aiki.

Comments (0)
Add Comment