An Gurfanar Da Wani Mutum A Gaban Kotu Kan Kashe Ƙaninsa Ɗan Shekara 6

An kai wani mutum mai suna Kingsley Bassey gidan gyaran hali na Kirikiri bisa zargin kashe ƙaninsa ɗan shekara shida lokacin da yake cikin maye.

Ƴansanda ne suka gurfanar da mutamin ɗan shekara 23 a duniya a gaban Kotun Majistare ta Yaba gaban Alƙali Patrick Nwaka kan zargin kisan kai.

Mai shigar da ƙara, Thomas Nuruddeen ya faɗawa kotun cewa, wanda ake zargin, ya aikata laifin ne ranar 29 ga watan Mayu, 2023 da misalin ƙarfe 8:30 na safe a gida mai lamba 3, kan titin Poultry Road da ke Meiran a Jihar Lagos.

Nuruddeen ya bayyana cewa, laifin da Kingsley ya aikata ya saɓa da Sashi na 222 wanda aka tanadi hukuncinsa a sashi na 223 na Dokar Manyan Laifuka ta Jihar Lagos ta 2015.

Nuruddeen ya roƙi kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake zargin har zuwa lokacin da za a samu rahoton binciken Hukumar Kula da Gurfanar da Mutane.

Alƙalin Majistaren ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari na Kirikiri, sannan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Agusta, 2023.

Jihar LagosKisan kai
Comments (0)
Add Comment