Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya faɗawa sanatoci cewar, Magatakardar Majalissar Tarayya zai tura musu wasu kuɗaɗe a asusunsu na banki domin su ji daɗin yin hutun da zasu shiga.
A wani bidiyo da ya zagaya yanar gizo a yau Laraba, an ga Akpabio yana faɗin maganar kafin a gabatar da ƙudirin ɗage zaman a ƙarshen zaman na yau.
Shugaban ya ce, “Saboda mu ji daɗin hutunmu, magatakardar majalissa ya tura abun hasafi cikin asusun bankunanmu.”
A nan ne wasu daga cikin sanatocin suka farkar da Akpabio cewar ana fa haska zaman nasu su kai tsaye a duniya.
Daga nan ne kuma sai shugaban ya yi wata maganar da take nufin janye waccan ta baya, inda ya ce, “Na janye waccan maganar.”
Akpabio ya ɗora da cewa, “Saboda ku ji daɗin yin hutunku, Shugaban Majalissar Dattawa ya tura addu’o’i cikin akwatunan saƙonku domin ya temakeku tafiya da dawowa lafiya.”