An Kafa Kwamitin Da Zai Jagoranci Tallafawa Matan Jigawa A Fannin Tattalin Arziƙi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙaddamar da wani kwamiti mai mahimmanci da ake kira Multi-Sectoral Coordination Steering Committee domin jagorantar aiwatar da shirin Nigeria for Women Programme (NFWP), wani haɗin gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da nufin ƙarfafa tattalin arzikin mata.

Gwamna Malam Umar Namadi, yayin kaddamar da kwamitin a Dutse, ya bayyana cewa “Shirin NFWP wani taimako ne daga Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya domin inganta rayuwar mata da bunƙasa tattalin arzikin su,” yana mai cewa shirin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatinsa na kawar da matsalolin da ke hana ci gaban mata.

Gwamnan ya ce zai jajirce wajen tabbatar da nasarar shirin domin “magance matsalolin da suka danganci cibiyoyi da kasuwanni da ke hana mata shiga harkokin bunƙasa tattalin arziki.”

KARANTA WANNAN: Na Ceto Tsarin Fanshon Jigawa Daga Rugujewa – Gwamna Namadi

Hajiya Hadiza Abdulwahab, kwamishinar harkokin mata kuma shugabar kwamitin, ta bayyana godiya ga gwamnan bisa wannan amanar da ya ba su, tana mai cewa, “Za mu ba da dukkan goyon baya don tabbatar da nasarar wannan shiri.”

Cikin wata sanarwa daga Kakakin Gwamna, Hamisu Gumel, an bayyana cewa kwamitin zai jagoranci tsara manufofi, daidaita aikace-aikace tsakanin ma’aikatun gwamnati, da tabbatar da cewa shirin na tafiya da burin cigaban jihar Jigawa.

Mambobin kwamitin sun hada da kwamishinoni daga ma’aikatun kuɗi, tsare-tsare da tattalin arziƙi, lafiya, noma, ilimi, ruwa da ƙananan hukumomi tare da Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Mata da kuma Sakatare na Musamman ga Gwamna.

Kwamitin zai duba da amince da tsarin aikin shekara da kasafin kuɗi, ƙarfafa haɗin kai a ƙananan hukumomi, da tallafa wa kungiyoyin mata da kuma sa ido kan yadda shirin ke tafiya a faɗin jihar.

Comments (0)
Add Comment