An kama wasu ƴan ƙungiyar Boko Haram da ake zargi da kitsa kai hari garin Yola, Jihar Adamawa gidan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
Wani wanda ake zargin mai shekaru 29 a duniya, Jubrila Mohammed, wanda ya amsa cewar shi ɗan Boko Haram ne daga Domboa a Jihar Borno, an kamashi ne a ƙofar gidan Atiku lokacin da yake ƙoƙarin kai harin da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Lahadin da ta gabata.
Bayan an kama shi ne, aka kuma samu nasarar kama wasu abokan aikinsa su su uku.
A wata sanarwa, Ofishin Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023 ya ce, ya sanar da al’ummar Najeriya cewa, a ranar Lahadi dai-dai misalin ƙarfe 9:44 na dare an kama wani mutum da yake neman a kwatanta masa gida Atiku Abubakar a Yola.
Sanarwar ta ƙara da cewa, bayan kama mutumin da ake zargin, an miƙa shi ga jami’an ƴansanda, inda daga bisani ya tona asirin abokan aikinsa su uku waɗanda aka samu nasarar kama su daga baya.
An miƙa dukkan waɗanda ake zargin ga rudunar sojoji domin faɗaɗa bincike.