An Kama Ɗan Shugaban Boko Haram A Chadi, Ana Zargin Yana Jagorantar Ƙungiyar Ƴan Ta’adda

A Chadi, jami’an tsaro sun kama wani matashi da ake zargin ɗan marigayi Mohammed Yusuf ne mai suna Muslim Mohammed Yusuf, tare da wasu biyar da ake zargin su membobin wata ƙungiyar ƴan ta’adda ne a yankin Tafkin Chadi.

Wata majiyar leƙen asiri a yankin ta shaida wa AFP a ƙarshen mako cewa, “Ƙungiyar ta kasance ƙarƙashin jagorancin Muslim, ƙaramin ɗan marigayi Mohammed Yusuf.”

Majiyar ta kuma bayyana cewa ƙungiyar ta kasance wani reshen ƙungiyar ISWAP, reshen da ya fice daga Boko Haram saboda bambancin aƙida.

Hotuna da AFP ta gani sun nuna saurayi mai siffa kamar Muhammad Yusuf cikin wando mai launin shuɗi yana tsaye kusa da manya, kuma ana cewa yana amfani da sunan bogi Abdrahman Mahamat Abdoulaye yayin da aka danganta shi da Habib Yusuf (Abu Mus’ab Al-Barnawi).

Tsohon kwamandan Boko Haram wanda ya tuba ya ce shi da tawagarsa “su shida ne aka kama,” yayin da kakakin ƴan sandan Chadi, Paul Manga, ya bayyana cewa an kama “‘yan fashi da ke aiki a cikin birni… ba su da takardu, su mambobin Boko Haram ne.”

An ce an kama ƴan ƙungiyar ne “a wasu watanni da suka gabata,” amma hukumomin leƙen asiri da ƙungiyoyin yaƙi da ta’addanci na Najeriya ba su maida martani kai tsaye ba game da wannan iƙirari.

Wannan kamun ya nuna sabuwar damuwa ga tsaron yankin Tafkin Chadi, inda rikice-rikicen ta’addanci suka ɗauki wani sabon salon sarƙaƙiya a ƴan shekarun nan.

Comments (0)
Add Comment