An Kama Manajan Gidan Mai Da Wasu Mutane Bisa Zargin Aikata Fashi

Rundunar ƴan sanda a Legas ta kama wasu mutum huɗu da ake zargi da shiga cikin wani gungun ƴan fashi da makami da ke addabar wasu sassan birnin, ciki har da wani manajan gidan mai.

Rahotanni sun ce, an cafke su ne a yankin Ejigbo bayan samun bayanan sirri da kuma bincike na musamman daga ɓangaren jami’an tsaro.

Ɗaya daga cikin jami’an ya bayyana cewa: “Manajan gidan man yana cikin waɗanda aka kama, yayin da mai gidan man bai san shi da aikata irin waɗannan laifukan ba, kuma waɗanda ake zargin sun amsa cewa su ƴan fashi ne.”

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Tawagar Tactical Squad Hawk ce ta aiwatar da kamen, kuma ƙungiyar NUPENG ta taka rawa wajen kamo manajan.”

WANI LABARIN: NNPP Ta Ce Kwankwaso Ba Shi Da Damar Ƙara Yin Takara A Ƙarƙashinta

Wannan samame ya biyo bayan kama wani gungun masu fashi da ke sace manyan motocin mai da kaya a jihar, inda aka ce an gano motar mai da aka sace a unguwar Orile ba tare da mai ba.

A baya, rundunar ta ce ta kama mutum bakwai ciki har da Izuchukwu Nwanoruo da Kayode Falodun, tare da motar mai da aka yi amfani da ita wajen safarar man da aka sace.

“Dukkanin waɗanda ake zargin na taimaka wa rundunar da bayani yayin da ake ci gaba da bincike,” in ji Hundeyin, wanda ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda, Olohundare Jimoh, ya yaba da ƙoƙarin jami’an.

Rundunar ta shawarci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai a kan lokaci domin taimaka wa wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Comments (0)
Add Comment