Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Ondo ta cafke mutane uku da ake zargi da garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko.
Waɗanda aka sace sun haɗa da Omoniyi Eleyinmi, jami’in kula da harkokin gudanarwa na Kwalejin Ilimi, da wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.
Rahotanni sun ce Eleyinmi ya iso gida ne bayan kammala aiki, matarsa ta fito ta tarbe shi, amma ta tsere lokacin da ƴan bindiga suka buɗe wuta.
An tuntuɓi iyalan wanda aka sace sau biyu, inda aka buƙaci kuɗin fansa kafin a sako su a yankin Ago Panu na ƙaramar hukumar Owo.
Majiyoyi sun ce an biya kuɗin fansa kafin a sako su a ranar Lahadi.
Ƴan sanda sun ce sun kama waɗanda ake zargi a daji yayin da suke raba kuɗin fansar da suka karɓa.
Kakakin rundunar, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da cewa, “An miƙa su ga sashin yaƙi da garkuwa da mutane domin gudanar da cikakken bincike.”