An Kama Wata Mota Maƙare Da Makamai A Katsina

Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun kama wata mota maƙare da makamai masu yawan gaske a Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Kwamishinan Tsaro da Kula da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin Talata a garin Batsari.

Ya ce, bisa bayanan sirri da aka samu, jami’an tsaron sun tsayar da wata motar haya mai lamba BTR 45 XA, inda suka gano harsasai 610 na bindigar AK-47 da General Purpose Machine Gun (GPMG) tare da igiyar jigidar harsasai biyu da aka ɓoye a ƙarƙashin kujera.

Wani mutum da aka bayyana yana sanye da tufafin farin boyel ne ya ke da alhakin ɓoye waɗannan makamai, amma ya tsere yayin da aka tsayar da motar don bincike.

Mu’azu ya bayyana cewa, “mutumin ya nace kan zama a bayan motar tare da nuna damuwa da tsoro, kuma ya samu tserewa lokacin da aka tsayar da motar don yin bincike.”

Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba wa jami’an tsaron bisa jajircewarsu wajen kare al’umma, kuma Gwamna Dikko Radda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro don yaƙar duk wani nau’in laifi a jihar.

Jihar KatsinaMatsalar Tsaro
Comments (0)
Add Comment