An Kashe Sojojin Nijar 17 A Iyakar Ƙasar Da Mali

An kashe sojojin Jamhuriyar 17 a jiya Talata a wani hari da ake zargin ƴan ta’adda ne suka kai musu a iyakar ƙasar ta yamma wadda ta haɗa ƙasar da Mali, in ji Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar.

Ma’aikatar Tsaron ta ce, sojojin sun fuskanci ajalinsu ne a harin da waɗanda ake zargi ƴan ta’adda ne suka kai musu a garin Koutougou a jiya Talatar.

KARANTA WANNAN: Masu Juyin Mulkin Nijar Zasu Yankewa Bazoum Hukuncin Cin Amanar Ƙasa

Ta ce, bayan waɗanda suka mutu su 17, akwai kuma ashirin da suka samu raunuka, shida a cikinsu suna cikin mawuyacin hali, inda dukkansu aka kai su babban birnin ƙasar Niamey.

Sojojin sun ce, a faɗan da ya faru tsakaninsu da ƴan ta’addar, sama da guda 100 cikin ƴan ta’addar sun rasa rayukansu.

AFP

Jamhuriyar Nijar
Comments (0)
Add Comment