An Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnati 6 A Jigawa

A jiya Talata ne Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya amince da naɗin sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnati guda shida domin cike guraben da ake da su a jihar.

Sanarwar naɗin ta fito ne a takardar da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Jigawa, Alhaji Hussaini Ali Kila ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa sabbin Manyan Sakatarorin daraktoci ne da aka ciyar da su gaba.

Sabbin Manyan Sakatarorin sune, Musa Muhammad Yalleman, Muhammad Mahmoud Dawaki, Abdul Ibrahim, Isyaku Shehu, Ibrahim Adamu, da kuma Dr. Abdullahi Umar Namadi.

Alhaji Hussaini Ali Kila ya bayyana cewa, naɗin Manyan Sakatarorin an yi shi ne bisa duba cancanta, ƙwarewa da kuma halaye na gari, yayin da ya ƙara da cewa naɗin nasu ya fara aiki nan take.

Ku Karanta Wannan: Haɗakar Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma Ta Jigawa Ta Zabi Sabbin Shugabanni

Kwamishinan Shari’a na Jihar Jigawa, Barrister Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya rantsar da Manyan Sakatarorin yau a Fadar Gwamnatin Jihar Jigawa, a gaban Gwamna Umar Namadi.

Cikin waɗanda suka halarci bikin rantsuwar akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Engr. Aminu Usman; Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim Mamsa; Shugaban Ma’aikatan Jihar Jigawa, Alhaji Hussaini Ali Kila; Kwamishinoni da kuma Manyan Sakatarori na jihar.

A jawabinsa bayan gabatar da rantsuwa ga Manyan Sakatarorin, Gwamna Umar Namadi ya yi kira gare su da su kula da manufofin gwamnatinsa guda goma sha biyu da ya miƙawa kowanne kwamishina na jihar.

Ya kuma hore su da jajircewa da rikon amana a matsayinsu na waɗanda zasu kula da harkokin mulki na ma’aikatunsu.

Jihar JigawaManyan Sakatarorin Gwamnati
Comments (0)
Add Comment