Ma’aikatar Ilimi mai Zurfi, Kimiya da Fasaha ta Jihar Jigawa ta sanar da ranakun tantance waɗanda suka zana jarabawar neman aikin koyarwa na J-Teach a jihar.
Ma’aikatar ilimin ta rarraba ranakun gudanar da tantancewar zuwa yankunan ilimin da ake da su a jihar.
Ga bayanin gurare da ranakun da za ai tantancewar:
Alhamis 17/8/2023 za a yi wa Yankin Gumel da Babura a Gumel.
Juma’a 18/8/2023 za a yi wa Yankin Hadejia da Birniwa a Hadejia.
Asabar 19/8/2023 za a yi wa Yankin Kazaure da Ringim a Kazaure.
Litinin 21/8/2023 za a yi wa Yankin Jahun da Kafin Hausa a Jahun.
Talata 22/8/2023 za a yi wa Yankin Dutse da Birnin Kudu a Dutse.
A ko wacce rana za ana fara tantancewar ne da misalin ƙarfe 9 na safe, kamar yanda Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi mai Zurfi, Kimiya da Fasaha, Wasilu Umar Ringim ya faɗa.