An Samu Masu Dauke Da Kwalara Su 447 A Jihohi 6 Na Najeriya – NCDC

Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka Ta Najeriya, NCDC, ta ce, cikin mako biyar kacal, jihohi 6 na Najeriya sun sanar da samun masu dauke da cutar kwalara har mutane 447.

Jihohin sun hada da Cross River mai mutane 397, Zamfara mai mutane 25, Ebonyi mai mutane 11, Abia mai mutane 9, Bayelsa mai mutane 3 da kuma Kano mai mutane 2.

A shafinta na internet, NCDC a jiya Litinin ta wallafa cewa, jihohi 12 ne suka sanar da zargin samun cutar kwalara a cikinsu tun daga farkon shekarar nan ta 2023.

Jihohin sun hada da Abia, Bayelsa, Benue, Cross River, Ebonyi, Kano, Katsina, Niger, Ondo, Osun, Sokoto da kuma Zamfara.

Hjukumar ta ce, a daidai 5 ga watan March da ya gabata, an samu korafe-korafen samun cutar kwalara har guda 922 daga jihohin, ciki har da mutuwar mutane 32, wadanda suka hada da mutane 16 daga Cross River, 6 daga Abia, 6 daga Ebonyi, 2 daga Niger, 1 daga Zamfara da kuma wani 1 daga jihar Bayelsa.

Korafe-korafen da aka samu kan kamuwa da cutar ta kwalara ya fi karfi a kan maza da mata ‘yan sama da shekara 45 a duniya.

Kididdigar korafe-korafen, in ji NCDC ta nuna cewa kaso 54 na wadanda ake zargin sun kamu da cutar maza ne, yayinda kaso 46 suka kasance mata.

NAN

Cutar KwalaraNajeriyaNCDC
Comments (0)
Add Comment