An Yi Kira Ga JAMB Da Ta Sauƙaƙa Hanyar Yin Regularization Ga Masu Cike DE

Hukumar Shiraya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ce duk dalibin da ya zaɓi ya sami addmission ba ta ingantacciyar hanya ba zai fuskanci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da JAMB ke jaddada cewar, duk wani admission na shiga wata makarantar gaba da sikandire dole ne ya biyo ta ita.

Wannan kira dai da ya zo a shafin hukumar na X a yau Lahadi, ya zo ne a dalilin shawarar da wani ya bayar na JAMB ta kara inganta tsarin inganta bayanai domin shiga makarantu wanda ake kira da regularization.

Mutumin mai suna Adekunle Adu a manhajar X, ya yi kira ga JAMB da ta samar a shafinta wata dama ta yin regularization ba tare da mutum ya ziyarci ofishinta ba.

Sai dai a nata martanin, JAMB ta ce, irin wannan kiran ma bai kamata yana tasowa ba, saboda dole ne duk mai bukatar shiga wata makarantar gaba da sikandire ya bi ta hanyarta kafin ya shiga tun a farko.

Shi dai regularization na nufin inganta karatun da aka yi ba tare da admission daga JAMB ba zuwa wanda JAMB zata iya aminta da shi, kuma daliban da suka kammala Diploma OND da kuma wasu masu NCE ne ke yinsa domin samun damar yin degree ta hanyar DE.

Comments (0)
Add Comment