Ana Ayyukan Raya Ƙasa Ne A Inda Zasu Yi Amfani, Martanin Abdulaziz Abdulaziz Ga Kwankwaso

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan kafafen yaɗa labarai ɓangaren jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce gwamnatin Tinubu na gudanar da ayyukan tituna ne bisa la’akari da amfanin da zasu yi wa tattalin arziƙin ƙasa da ƴan ƙasa gaba ɗaya.

A wata hira da ya yi da Channels Television, ya musanta zargin Rabiu Musa Kwankwaso na cewa gwamnatin Tinubu tana fifita yankin Kudu wajen ayyuka da ke buƙatar manyan kuɗi.

Abdulaziz ya bayyana cewa, “Dole ne mu daina kallon ayyuka a matsayin na Arewa ko Kudu, mu fi mayar da hankali kan irin amfanin da suke da shi ga ƙasa baki ɗaya.”

WANI LABARIN: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Wata Jihar Arewa

Ya ce gwamnati ba ta nuna wariya ba wajen rabon ayyuka, yana mai misalta titin Sokoto zuwa Badagry da ke Arewa da titin Lagos-Calabar da ke Kudu a matsayin iri ɗaya.

Ya kuma musanta cewa an yi watsi da aikin titin Abuja-Kaduna-Kano, yana mai cewa an dawo da aikin yanzu haka kuma ana ci gaba da shimfiɗa hanyar.

“Abin da ya kamata a duba shi ne yadda waɗannan ayyuka ke taimakawa wajen haɓaka haɗin kai da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa,” in ji shi.

Ya kuma ƙarfafa cewa gwamnati na aiki ne don tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan yankunan Najeriya.

Comments (0)
Add Comment