Ana Matsawa Najeriya Kan Ta Amince Da Auren Jinsi

Cocin Angalican ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bijirewa kiraye-kirayen da Turawan Yamma ke mata na ta sake matsayinta kan auren jinsi a Najeriya.

Wannan dai na a cikin jawabin bayan taron da cocin ta saki bayan kammala taro na 12 na shugabannin cocin na faɗin Najeriya wanda aka gudanar a Abuja.

Takardar bayan taron, wadda Dr. Abraham Yisa da Babban Lauyan Najeriya, Odein Ajumogobia suka sanyawa hannu ta bayyana cewar, Najeriya na fuskantar matsi daga masu kare haƙƙin masu auren jinsi a duniya da kuma ƙasashen waje wajen ganin an halatta auren jinsi a ƙasar.

KARANTA WANNAN: Amurka Ta Cire Najeriya Daga Jerin Masu Tauye Damar Yin Addini

Takardar ta kuma yi kira ga mabiya addinin Kirista da su tabbata kan aikin imani da biyayya ga Ubangiji ta hanyar yin rayuwa wadda a cikinta a kwai gaskiya da mutunci sannan kuma ta yi kira ga cocuna da su yi riƙo da addinin gaskiya.

Takardar jawabin bayan taron ta kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su koma ga Allah domin neman ɗauki kan al’amuran ƙasa, inda tai nuni da cewar Allah yana tare da ƴan Najeriya a ko da yaushe.

Haka kuma ta yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai, da su koma ga Allah tare da watsi da dukkan abubuwan ƙi domin a samu ingantaccen ci gaba a ƙasa.

Auren JinsiNajeriya
Comments (0)
Add Comment